<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Doane, William Howard (1832-1915), Crosby, Fanny Jane (1820-1915)</author>
<title>Mu Yi Farin Ciki Mu Yi Murna Kuwa LW480</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mu yi farin ciki mu yi murna kuwa
 Don masu bin Yesu akwai nasara
 Zai fyauce mu duka mu ratse sammai
 Zai ciyadda ranmu da  itaccen rai.

[V2]
 KORUS
 Nasara, nasara zuwa dukan mu dai
 Nasara, nasara za mu ci ta sosai
 Mu zo mu bi Yesu mu yi anniya
 Zai ba mu ladanmu na har abada.

[V3]
 2) Ga can cikin sama a rubutace
 Suna na mai binsa kan farin dutse.
 Ba wanda ya sani sai shi mai karɓa
 Da Ubangijinmu Mai Cin Nasara.
 Korus

[V4]
 3)Wanda ya bi Yesu Mai Ceto kaɗai
 Za a ba shi tufafi da rawanin rai
 Zai zamna da Kristi a kursiyinsa
 Da murna mai yawa don yin nasara.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>480</hymn_number>
</song>